Help:Extension:UniversalLanguageSelector/Input methods/ha-tilde

This page is a translated version of the page Help:Extension:UniversalLanguageSelector/Input methods/ha-tilde and the translation is 100% complete.

A yanzu zaku iya rubutun Hausa da dukkan harrufanta!

Domin yin hakan, sai kubi wannan bayanin:

  1. Ku shiga akwatin nema da ke a saman shafin.
  2. Ku latsa alamar keyboard da zai fito a jikin akwatin nema.
  3. Idan "Hausa" ya fito a saman jerin sunayen, sa ku zaɓi "Hausa - tilde".
  4. Idan "Hausa" bai fito ba a cikin jerin sunayen, sai kubi bayani mai zuwa:
    1. Ku latsa alamar "..." dake a ƙasan jerin sunayen. Dan ƙaramin falle zai fito.
    2. Ku gano "Hausa" a cikin fallen. Ku latsa ta.
    3. Ku sake latsa alamar keyboard ɗinnan sannan ku zaɓi "Hausa - tilde".

Domin cire wannan keyboard na musamman, ku latsa alamar nan ta keyboard sannan sai ku zaɓi "Use native keyboard" ko kuma ta hanyar shortcut Ctrl+M. Domin sake kuma shiga wurin, sai ku latsa Ctrl+M, ko kuma ku sake bin hanyoyin da aka bayyana a sama.

Domin rubuta haruffan Hausa, ku latsa alamar tilde (~) daga nan sai ku latsa harafin Latin mafi kusanci da wannan harafin na Hausa. Misali, in kuna son ku rubuta ɓ, sai ku fara sa ~ da kuma b. Ga cikakken jerin su anan ƙasa:

To type this letter... Type these keyboard keys:
Ɓ ~B
ɓ ~b
Ɗ ~D
ɗ ~d
Ƙ ~K
ƙ ~k
~R
~r
Ƴ ~Y
ƴ ~y

Domin rubuta alamun dake akan haruffa, sai ku fara rubuta harafin, sannan sai tilde (~) sai kuma ku ƙara da /, \, ko kuma ^.

Domin rubuta wannan harafin... Ku rubuta wannan haruffan na kan keyboard:
à a~\
é e~/
ô o~^